An bude sabon gwamitin duba yuhuwar bude Makarantu a Kano.
1 min read
Kwamishinan Ilmi na jihar Kano Sunusi Majidadi ya kaddamar da yan kwamitin da zasu yi duba kan tsare-tsaren da ma’aikatar ilmi ta tarayya ta aikewa makarantun jihohi 36 domin bin ka’idojin dakile cutar COVID-19 kafin a bude makarantun.
Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun jami’in hulda da jama’a, Aliyu Yusuf ya aikewa Ayrah News Hausa.
Sakon ya bayyana cewar Kwamishinan ya nemi yan kwamitin su duba takardun da gwamnatin tarayya ta aiko domin bin ka’idojin da aka kafa.
Kwamitin dai ya samu shugabancin Comrade Dalha Isah Fagge akwai sauran manyan masana da shugabannin a bangaren harkokin ilmi na jihar kano da duk zasu kasance a ciki…
Ana sa ran zasu kammala aikin kwamitin cikin kankanin lokaci don haka ya bayar da damar fara karatu a jihar Kano..