June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kasar Saudiyya ta Sassaukata dokar kulle sai dai babu bayani kan aikin Hajji.

1 min read

Kasar Saudi Arabia ta sanar da shirin janye dokar zirga-zirga da ta sanya a sassan kasar, a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da dari biyu da talatin.

Wannan na cikin wata sanarwar da ma’aikatar harakokin cikin gida ta kasar Saudiyya ta fitar, inda ta ce daga yau Lahadi 21 ga watan Yuni da muke ciki za a janye dokar, ciki har biranen Makka da Jidda.

Rahotanni na nuni da cewa za a baiwa jama’a damar fitowa don gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Sai dai ya zuwa yanzu ba a kai ga sanya ranar fara saukar jiragen sama daga wasu kasashen ba, inda kuma sanarwar bata yi bayani karara kan batun aikin Umara ko Hajjin bana ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *