June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shaguna saba’in da Motoci 10 da dai-daitasahu 40 na mallaka da sana’ar Kunshi.

2 min read

Aisha Zahradden Isah mace ce wadda ke gudanar da sana’ar kunshi yau shekara 10.
Haka zalika ta kuma bayyana cewa ta fara gudanar da sana’ar ta da shago guda daya sai gashi yanzu tana da shago Saba’in Wanda ta mallaka da wannan sana.
Matashiyar ta kuma ce dukkan wannan nasara ta samu ne a sakamakon hakuri data yi da irin
matsalolin rayuwa data tsinci kanta a ciki a yayijn da take rainan shagonta.

Ta ce babu wani abu da za’a sameshi batare da ansha wahala ba l, wanda a karshe dadi ya kan samu.

A yanzu haka ina da baburan Adai-daita sahu 40 da kuma motoci kirar Golf guda
Goma.

Aisha Zahradden ta kuma ce tana da ma’aikata 150 Wanda suke gudanar mata da kasuwancin ta.

Ko da aka tambayeta matsayin karatu sai ta ce tayi degree dinta na farko a Jami’ar Alkalam dake jihar Katsina inda ta karanci aikin Jarida a jami’ar Alkalam.

Matashiyyar ta kuma bayyanawa Jaridar Bustandaily cewa babbar matsalar matasan kasar nan bai wuce raina sana’a ba inda ta kuma bukaci ‘yan uwanta mata dasu dage su nemi na kasan su musamman ma a wannan zamani mai cike da kalubale kala-kala.

Matashiyar dai ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da Jaridar Bustandaily a yau Lahadi.
Aisha kammala Degree na dinta a a jami’ar alkalam dake jihar Katsina inda ta karanci fannin aikin jarida a jami’ar dake jihar ta Katsina.
Sai matashiyar ta kulubalanci mata da zama kai batare da tashi tsaye ba,wajen neman nakan su ba.
Ta kuma bukaci matasa dasu daina raina sana’a komai kankantar sana’a.

Aisha ta Kara kira ga matasan Nigeria dasu sani cewa aikin gwamnati baya samuwa a hanlinsu yanzu cikin sauki musamman ma hakidar nan ta sai Dan wane da wane ne ake baiwa aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *