June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin somalia na gudanar da zanga-zanga kan albashi.

1 min read

Wasu sojojin da ke bore a Somaliya sun tare babban titin da ke kusa da fadar shugaban kasar, a wani mataki na zanga -zanga saboda kin biyan su albashi.

Wasu daga cikin sojojin sun ce sun shafe shekara daya ba tare da albashi ba.

Wata kafar yada labarai ta kasar ta nuna wani hoton bidiyo yadda sojoji ke tare masu abin hawa daga dakarun kwantar da tarzoma na kungiyar Afrika daga wucewa.

Sojojin ne dai ke fafatawa da mayakan al-Shabab masu tsattsauran ra’ayin addini, wadanda suka yi ikirarin daukar alhakin wasu tagwayen hare-hare da aka kai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *