Wata Babbar Tankar mai ta kama da Wuta a Jihar Legas
1 min read
Wata tankar mai ta kama da wuta a kan wata babbar gada da ake kira Kara bridge a Legas kudancin Najeriya.
Rahotanni sun ce wutar ta yadu inda ta sake kama wata tankar mai da ke kusa da ita mai dauke da fetir.
Tuni dai ‘yan kwana-kwana suka isa wajen domin kashe wutar da rahotanni suka ce ta ci motoci da gidajen da ke kusa.
Zuwa yanzu ba a tantance musabbabin faruwar lamarin ba, da kuma hasarar rayuka da dukiyoyi da fashewar ta janyo.