September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yanzu -yanzu aka rushe ofishin Jakadancin Nigeria dake Kasar Ghana.

1 min read

An rusa ginin ofishin jakadancin Najeriya da ke Ghana

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar da ke Accra, babban birnin Ghana.

Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

“Muna yin tir da hare-hare biyu da masu aikata laifi da ba a san ko su wane ne ba suka kai a wani gida da ke ofishin jakadancinmu a Accra, Ghana inda aka yi amfani da babbar motar rusa gini wajen rusa gidan,” in ji Mr Onyeama.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da takwararta ta Ghana kan batun kuma ta bukaci a dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.

Ya bukaci a bayar da cikakken tsaro ga ‘yan Najeriya da kadarorinsu da ke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *