A Kasar Brazil Fiye da mutum 50,000 sun mutu a sakamakon Covid 19.
1 min read
Brazil ta zama kasa ta biyu bayan Amurka da fiye da mutum 50,000 suka mutu a sanadiyyar annobar korona, kuma cikinsu mutum 641 ne suka rasa rayukansu cikin sa’a 24 da ta gabata kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar.
Kasar ta kuma sami wasu mutum 17,459 da suka kamu da cutar a ranar Lahadi kawai – inda masu dauke da cutar suka zarce miliyan daya a karon farko a kasar.
Brazil ta kafa tarihi a karo biyu – tarihi na kaurin suna wanda babu mai son kafa irinsa.
Amma duk da wannan koma bayan, Shugabn kaar Jair Bosonaro ya ki sauya manufofinsa – inda ya daina cewa uffan game da wadanda suka mutu.
A madadin haka sai nanata wani kira yake yi cewa tilas kasar ta koma bakin aiki domin tattalin arzikin kasar ya farfado.