March 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dalilin da yasa muka ga dacewar gina Ruga ta zamani da ta lakume makudan kudi – Jibrilla Muhammad.

4 min read

Dalilin da yasa muka ga dacewar gina Ruga ta zamani da ta lakume makudan kudi – Jibrilla Muhammad.
Manajan daraktan hukumar zuba hannayen jari ta jihar Kano Dr. Jibrila Muhammad, ya ce matakin gina gidaje da Gwamnatin Kano tayiwa al’ummar Fulani makiyaya, zai taimaka wajen dakile fitintinu tsakaninsu da takwarorin su manoma.
Dr. Jibrilla Muhammad wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin gina Ruga ta zamani da aka yi a Dajin Dansoshiya, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da wakilin Ayrah News Umar Idris Shuaibu.
Ya ce idan aka yi duba akan rayuwar Fulani makiyaya suna taimakawa tattalin arzikin Najeriya, wajen samar da madara da nama daga dabbobinsu.
“Albarkatun da makiyaya kan samar a kasar nan ba zai misaltu ba, kasancewar a kowacce rana ana yin amfani da nama a kowane bangare na Najeriya, wanda suke samar da kashi 85 cikin dari na dabbobin da ake yankawa don amfani da su a mayankun mu.
“Haka zalika idan ka dauki madarar shanu da Kindirmo da Nonon da matan Fulani ke shigo da shi garuruwa don amfanin yau da kullum, ana amfani da shi a matsayin abinci, kuma yana kara inganta lafiya saboda dimbin sinadaran da yake kunshe da shi.”
Dr. Jibrilla Muhammad ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta duba dimbin alfanun da suke karawa tattalin arzikin Kano, shi yasa ta dauki wannan mataki na samar musu mazauni na da ya kunshi abubuwan more rayuwa.
“Rugar Dansoshiya ta kunshi gidajen zaman makiyaya da asibitin dabbobi dana mutane, da kuma kasuwar siyar da albarkatun da suke samarwa.
Kasancewar tsaro na da muhimmancin gaske ga rayuwar dan Adam, mun dauki gabarar samar da ofisoshin jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda dana rundunar tsaro na Civil Defence.”
Manajan daraktan hukumar zuba jari ta jihar Kano ya ce wannan kokari da Gwamnatin Kano tayi, ya zama irin sa na farko a tarihin kasar nan da wata Gwamnati tayiwa Fulani makiyaya gata, wanda shakka babu zai bunkasa rayuwarsu, kana ya rage yawan matsaloli da kan auku tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Jibrilla Muhammad ya jaddada cewa, Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ga dacewar yin irin wannan gagarumin aiki ne, bayan tattaunawa da kungiyoyin ci gaban Fulani Makiyaya na Fuldan da Jowrows da dai sauransu, inda suka bada shawarwari yadda za a fara gudanar da aikin.
Idan ba a manta ba dai, a ranar 18 ga watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2019 ne Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamitin samar da Rugar irinta ta farko, karkashin jagorancin Manajan daraktan hukumar zuba jari ta jihar Kano Dr. Jibrilla Muhammad, sai sakataren kwamiti Umar Liman da kuma mambobin kungiyoyin Fulani da suka hadar da Idris Shuaibu Bayero daga kungiyar Jowros da Zubairu Ibrahim daga Miyetti Allah a matsayin mambobi, da dai sauran su.
Kwamitin bayan fara aiki ya zagaya makiyayu da ake da su a fadin jihar Kano don duba inda ya kamata a fara gabatar da wannan aiki, da suka hadar da Dajin Fanyabo cikin karamar hukumar Doguwa da Duddurun Gaya dake Ajingi, sai Dansoshiya dake karamar Kiru wanda aka yi wannan ginin Rugar ta zamani a yanzu da dai sauransu.
Dadin dadawa kwamitin ya bada rahoton inda ya kamata a samar da katafariyar kasuwar siyar da Madara da nono ta din-din-din a cikin kwaryar birnin Kano, don baiwa dimbin jama’ar dake sana’ar siyar da Nono a kasuwar Kofar Wambai damar gudanar da kasuwancin su cikin kwanciyar hankali da tsafta.
“Dayawan lokuta babu cikakkiyar tsafta a wuraren da ake hada-hadar siyar da Madara da Nono, wanda Gwamnati tayi tsari da zamu samar musu da waje da yake da tsafta, kana kuma mu tallafa musu da na’urorin alkinta albarkatun Nono don kada ya rinka lalacewa cikin karamin lokaci.”

Dr. Jibrilla Muhammad ya ce manufar yin wannan katafaren aiki, bai wuce tsugunar da Makiyaya ba don kaucewa matsalolin da yawon da suke yi yake zuwa da shi, musamman a yankunan Kudancin kasar nan.
“Idan ka duba Fulani na fuskantar barazana a dalilin zuwan da suke yi yankunan Kudancin Najeriya, da aka fi samun dausayi da dabbobi ke bukata a kowane lokaci musamman lokacin rani, to mun yi tsari ta inda zamu samar musu da ciyawa da dabbobin su za su rinka ci ta zamani.
A baya Gwamnatin Kano ta tura ‘ya’yan Fulani Makiyaya guda 60 kasar Turkiyya, don koyo yadda ake yin bayen shanu da kuma rainon irin wannan ciyawa, muna sa ran amfani da wadannan matasa wajen inganta rayuwar ‘yan uwansu.” A cewar Jibrilla.
Ya kara da cewa wanna tsari, zai baiwa dimbin al’ummar Fulani damar zama waje daya, don amfana da arzikin da ke tattare da su, kuma su samu damar sanya ‘ya’yan su a makaranta kamar kowa.
Dr. Jibrilla Muhammad ya kuma ja hankalin shugabannin kungiyoyin ci gaban Fulani, da su maida hankali wajen ganin makiyayan sun alkinta wannan waje da Gwamnati ta kashe makudan kudade, don amfanin kansu dama al’ummar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *