September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dole a kawo karshen rikicin jam’iyyar APC iji Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria.

2 min read

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce za a shawo kan rikicin jam’iyyar ne kawai idan aka yi biyayya ga tanade-tanaden kundin tarin mulkinta.

Ya bayyana haka ne bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Lahadi.

A sakon da Ahmad Lawan ya wallafa bayan ganawar, ya ce “na yi amannar dole mu duba kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu sannan mu ga yada za mu magance wadannan masaloli. Kuma a yayn da muke yin wannan duba, ya zama wajibi mu hana rikicin ya ci gaba da faruwa.

Ya kara da cewa “ina so na tabbatarwa dukkan mambobin jam’iyyarmu cewa da yardar Allah, nan da kwanaki kadan, za mu ga yadda za a dauki matakin shawo kan rikicin”.

Rikicin APC ya sake tabarbarewa ne bayan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya fice daga jam’iyyar sakamakon takaddamar da ke tsakaninsa da shugabanta da kotu ta dakatar, Mr Adams Oshiomhole.

Hakan ya sa jam’iyyar ta nada tsohon gwamnan jihar Oyo wanda shi ne shugabanta na yankin kudancin kasar, Abiola Ajimobi, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar APC.

Amma wani fitaccen dan jam’iyyar Victor Giadom ya samu izini daga kotu cewa ya shugabanci jam’iyyar a matsayin riƙo, lamarin da masu fashin bakin siyasa suka ce zai hana jam’iyyar lashe zaben 2023 idan ba ta dinke barakar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *