July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

ECOWAS na goyon bayan takarar Ngozi Okonjo-Iweala

2 min read

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma Ecowas, ta goyi bayan takarar Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar wadda ministan harkokin wajen Najeriya Geoffery Onyeama ya wallafa a shafinsa na tuwita, ta ce Dakta Ngozi za ta jagoranci kungiyar ne daga shekarar 2021 zuwa 2025 idan aka zabe ta.

Sanarwar ta kara da cewa Najeriya ce ta mika sunan ‘yar takarar bayan la’akari da aka yi da kwarewarta a fannin ilimi da kuma bangaren aiki kan abin da ya shafi tattalin arzikin Najeriya da zamanta ministar harkokin kudi a 2003 da kuma 2011.

Shugabannin kungiyar cinikayya ta duniya sun lura cewa babu wani dan Afrika da ya taba jagorantar kungiyar tun bayan kafa ta a ranar 1 ga watan Janairun 1995, kamar yadda sanarwar ta zayyana.

Shugaban kungiyar kasuwanci ta cikin sanarwar ya ce an bude karbar sunayen ‘yan takarar ne daga ranar 8 ga watan Yuni da muke ciki kuma za a rufe karbar a ranar 8 ga watan Yuli mai kamawa.

Kungiyar Ecowas ko kuma Cedeao ta yi kira ga sauran kasashen Afrika da wadanda ma ba na nahiyar ba da su goyi bayan takarar tata.

Misis Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko da ta fara zama ministar kudin Najeiya da kuma ministar harkokin waje a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2006.

Tsohuwar ministar ta taba yin aiki da Bankin Duniya, inda ta shafe fiye da shekara 20 a hedikwatarsa da ke birnin New York na Amurka.

Ko a kwanakin baya ma sai da kamfanin sada zumunta na tuwita ya nada Dakta Ngozi a matsayin daya daga cikin manyan daraktocinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *