Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce shugabancin kama karya ka iya haifar da annobar Corona.
1 min readHukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadi kan rashin shugabanci a yayin da ake tsaka da annobar korona.
“Duniya tana cikin halin da take bukatar hadin kai na kasa da ma na duniya. Siyasantar da annobar korona ya ta’azzara yaduwarta,” a cewar shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, a wani taro ta intanet da ya yi da ma’aikatan lafiya ita ce matsalarmu.”
WHO ta kara da cewa cutar tana ci gaba da yaduwa kuma za a ga tasirin da ta yi kan tattalin arziki da sauran fannonin rayuwa shekaru aru-aru masu zuwa.
Mutum kusan miliyan tara cutar ta kama kuma ta yi ajalin kusan mutum 470,000.