Kasar Ghana ta kafa kwamitin bincike kan kan rushe Ofishin jakadancin Nigeria.
1 min read
Ma’aikatar wajen Ghana ta soma bincike kan rusa wani gina da ke ofishin jakdancin Najeriya da ke Accra, babban birnin kasar.
Ranar Asabar Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar.
Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, inda ya bukaci Ghana ta dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.
Mataimakin ministan wajen Ghana Charles Owiredu, ya shaida wa BBC Pidgin cewa “abin da ya faru abin takaici ne; Bai kamata mutum ya shiga ofishin jakadanci ba ba tare da an gayyace shi ba kuma Ghana ce take da alhakin kare lafiyar ma’aikatan difilomasiyya