September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutanan Kasar Saudiya ne kawai zasu gudanar da aikin Hajjin bana.

2 min read

Mahukuntan Saudiyya sun ce mazauna kasar ne kadai – cikinsu har da ‘yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta – za a bari su yi aikin Hajjin bana.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar aikin Hajji kasar ta fitar ta ce sun dauki mataki ne bisa la’akari da yadda cutar korona ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya.

Ga rashin riga-kafin annobar da ake fama da ita a duniya da kuma bukatar tabbatar da tazara tsakanin mutane da hana taron jama’a duka wadannan na daga cikin dalilan da ya sa aka soke Umara a bana, in ji sanarwar.

Sanarwa ta kara da cewa yadda cutar ke ci gaba da yaduwa da kuma yadda aka gaza samar da wata mafita in ba tabbatar da tazara tsakanin mutane ba, ya sa kasar za ta amince a yi aikin hajjin bana amma da ka’ida.

Ta ce aikin hajjin shekarar 1441 H/ 2020 D/ zai dauki mutanen da suke zaune a kasar ne kawai wadanda dama na zaune a saudiyya.

Saudiyya ta ce za a yi aikin hajjin tare da bin duk wasu hanyoyin da aka zayyana na kare mutane daga kamuwa da wannan annoba.

Za a bayar da tazara yayin aikin Hajjin kuma za a gudanar da shi kan doron koyarwar addinin musulunci kamar yadda aka saba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *