July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Novak Djokovic na fuskantar suka saboda gasar da ya shiry

1 min read

Shahararren dan Tennis dinnan na duniya Novak Djokovic na shan suka bayan da mutane hudu suka kamu da cutar Korona a gasar da ya shirya.

Djokovic ne na daya a wasan Tennis a duniya, kuma ya shirya wasanne da nufin bai wa yan wasa damar motsa jiki, bayan dadewa ba su buga wasa ba saboda annobar Korona.

Daga cikin wadanda suka kamu akwai yan wasa biyu wato Grigor Dimitrov da kuma Borna Coric.

Sauran kuma masu horar da yan wasa ne da kawo yanzu ba a bayyana sunayensu ba.

An lura cewa ana rungumar juna da kuma gaisawa a tsakanin ‘yan wasa, wanda hakan ya nuna ba a kiyaye ba da tazara ba tsakani.Article share tools

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *