April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar ‘yan Sandan Nigeria ta ce to wasu ‘yan kasar Philippines daga hannun bata gari.

2 min read

Rundunar `yan sandan Njaeriya ta ce ta yi nasarar ceto wata mata `yar kasar Philippines daga hannun wani dan Najeriya da ake zargin mayaudari ne.

Wanda ya tsare ta a gidansa na tsawon watanni, bayan ta kai masa ziyara da sunan soyayya.

Rundunar `yan sandan reshen jihar Enugu ta yi nasarar ceto ta ne, bayan an tsegunta ma ta inda aka kulle ta.

Matar `yan kasar Philippines mai suna Irene Torento Panas, `yan shekara 40 da haihuwa ta daka-gari ne daga kasarta zuwa kauyen Neke-Uno da ke karamar hukumar Enugu ta gabas, da ke jihar Enugu, a kudu-maso-gabashin Najeriya.

Ta kuma je ne da zummar rai zai ga rai, wato za ta yi tozali da masoyinta. Chukwudi Odo, dan shekara 54, bayan sun kulla abotarsu ta shekara biyu ta dandalin sada zumunta na facebook, inda suka yi ta yin zancensu ta hanyar tura wa juna sakonni, wato tun a ranar 8 ga wata Maris na 2017, ashe ashe…rabon wahala… Irene Torento Panas ta dauki kara da kiyashi!

Cikin wata sanarwa, Kakakin rundunar `yan sandan Najeriya, Frank Mba ya ce Irene Torento dai ta amsa gayyatar abokin nata ne cewa za ta kai masa ziyarar kwana goma a gidansa a Najeriya, kuma ta isa Najeriyar a ranar 22 Ga Watan Nuwamban bara, amma tana isa sai ya garƙame mata kofa ya hana ta komawa kasarsu, sannan ya datse duk wata hanyar da za ta yi magana da `yan uwanta.

Haka ta zauna har tsawon wata shida ba ta jin duniyar `yan uwanta. Su ma ba sa jin tata duriyar.

Binciken da `yan sanda suka yi ya gano cewa da niyya masoyi ko mayaudarin nata, wato Chukudi Odo ya yi wa buduwar ta sa shigo-shigo-ba-zurfi domin ya ci zarafinta a zaman da suka yi ta hanyoyi da dama, ciki har da lalata da ita, da kuma damfararta, ko cinye mata wasu `yan kudadenta.

Ko a lokacin da `yan sanda suka cece ta, sun same ta a halin rashin lafiya, don haka ne ba su ɓata lokaci ba suka wuce da ita asibiti.

Su ma `yan sandan, kamar yadda kakakinsu yake cewa wasu mutanen kauyen Neke-Uno din ne suka tsegunta musu wurin da ake boye matar, kana suka kai samame, suka kubutar da ita.

A halin da ake ciki dai, rundunar `yan sandan ta ce ta tuntubi ofishin jakadancin kasar Philippines da ke Najeriya da nufin bin matakan hada matar da `yan uwanta.Tsallake Twitter wallafa daga @PoliceNG

2 thoughts on “Rundunar ‘yan Sandan Nigeria ta ce to wasu ‘yan kasar Philippines daga hannun bata gari.

  1. wannan shine bambamcin musulmi da kirista . Amana ko Dan taji wata tazo burin sulaiman ta zauna lpy. to Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *