June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan kwallon kafar Serbia sun kamu da cutar koronavirus.

1 min read

‘Yan wasa biyar na tawagar kwallon kafar Serbia, Red Star Belgrade, sun harbu da cutar korona.

Sanawar da kungiyar kwallon kafar ta fitar ranar Litinin na zuwa ne bayan tawagar ta fafata a gasa da dama a kusa da dandazon ‘yan kallo.

Sauran kungiyoyin kwallon kafa – ciki har da gasar Premier ta Ingila – sun yanke shawarar komawa wasa ba tare da ‘yan kallo ba.

Da farko gwamnatin Serbia ta dauki irin wannan mataki, amma a farkon watan nan, ta amince a yi wasa a gaban ‘yan kallo.

Akalla ‘yan wasa hudu cikin biyar da ska kamu da cutar ba su yi wasan da aka yi ranar Asabar ba, saboda sun ji alamun kamuwa da cutar, in ji kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *