June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Birtaniya za ta buɗe wuraren shakatawa da na abinci.

1 min read


Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya ce za a bude gidajen abinci da
na shakatawa a Ingila daga ranar 4 ga watan Yuli.
Ya fada wa majalisa cewa daga tazarar mita biyu za a dawo mita daya
a inda ya zama dole a ba da tazarar.
To amma ya ce dole ne masu sana’o’i su dauki matakan kariya daga
cutar Korona.
To sai dai sassaucin bai shafi gidajen rawa ba da na motsa jiki.
Wannan shi ne sassauci da aka fi maraba da shi a Ingila tun bayan
kakaba dokar kulle a watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *