June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar aikin Hajji ta Nigeria Nacon zata mayarwa maniyyata aikin hajjin bana kudadensu.

3 min read

Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta ce za ta yi wani taro a ranar Talata, don sanin mataki na gaba da za ta ɗauka, bayan Masarautar Saudiyya ta sanar da jingine aikin hajjin bana ga maniyyatan ƙetare.

Ta ce duk da shawarwarin hukumomin Saudiyya a watan Maris, na a dakatar da shirye-shiryen aikin hajjin bana, a Najeriya, an ci gaba da wasu shirye-shiryen ibadar ta shekara-shekara.

“Tun watan uku da muka ga haka, mu ba mu so a ce mu daina (shirye-shirye) kwata-kwata ba. Saboda kada a zo daga baya a ce za a yi wannan aikin hajji, kuma a yi mana ba-zata,” in ji hukumar.

Kwamishinan ayyuka a hukumar, Alhaji Abdullahi Magaji Harɗawa ya ce matakin na ƙasar Saudiyya bai zo musu da mamaki ba, duk da yake sun shafe tsawon watanni a cikin zulumi.

Ya ce ko da yake, su ba su kai ga yanke hukunci ba, amma ganin wasu ƙasashe sun fara bayyana aniyarsu ta janyewa daga halartar aikin hajjin bana, su ma tuni suka fara yunƙuri don sanin abin yi.

Abdullahi Harɗawa ya ce tuni kuma suka tattara bayanai tare da gabatar da rahoton farko ga gwamnati don sanin matakin da za ta ɗauka, kafin zuwan wannan sanarwa daga Saudiyya.

“Duk shirye-shiryenmu, mun ɗora su ne a kan tunanin ƙila-wa-ƙala. Idan za a yi aikin hajji, ga matsalolin da za a iya fuskanta ga kuma yadda za mu shawo kansu. Idan kuma ba za a yi ba, ga abin da ya kamata a yi.

Duk su ne (bayanan) da muka riƙa tattarawa don gabatar wa gwamnati shawara saboda ta ɗauki matsaya a kan batun,” in ji Kwamishinan ayyukan hajji.

Ya ce yanzu kuma da aka samu wannan sanarwa, za su gudanar da taro ranar Talata don fitar da matsaya.

Abdullahi Magaji Harɗawa ya ce babu wani Musulmi da zai ji daɗin wannan mataki na janye damar zuwa aikin hajji ga maniyyatan ƙasashen waje.

“Idan ka yi la’akari da abin da ke faruwa, ai ba laifin Saudiyya ba ne. Ba kuma laifin kowacce ƙasa ba ne. Haka Allah ya ƙaddara, kuma ba yadda aka iya. Dole a karɓi ƙaddara,” in ji shi.

A cewarsa, ba abu ne na farin ciki ba ga gwamnatin Saudiyya da ta ce ta dakatar da aikin hajjin.

Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajjin Saudiyya ta fitar na cewa sun dauki matakin ne bisa la’akari da yaɗuwar cutar korona zuwa kasashe fiye da 180, da kuma yawan mutanen da cutar ta kashe.

Ta kuma kafa hujja da rashin samo wata allurar riga-kafin wannan annoba da kuma buƙatar tabbatar da tazara da taƙaita tarukan jama’a.

Saudiyya ta ce tanade-tanaden aikin hajjin shekarar 1441 H/ 2020 D/ za su ɗauki mutanen da ke zaune a ƙasar ne kawai. A cewarta za a yi aikin hajjin ne cikin bin duk ƙa’idojin kare mutane daga kamuwa da cutar kobid19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *