June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu ta dakatar da jam’iyyar PDP daga shirya babban taronta a Kano.

1 min read

Wata babbar kotun tarayya a jihar Kano ta bada umarnin dakatar da jam’iyyar PDP daga shirya zaben shugabannin kananan hukumomin Kano dana jihar.

Jaridar Solacebase ta ruwaito Alkali mai Shari’a Lewis Allagoa ne ya dakatar da babban Sufeton ‘yan sanda da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), daga sahalewa jam’iyyar zaben shugabannin, har sai an yanke hukunci kan karar da wani Ali Baffa da wasu mutane biyu suka shigar gaban kotun, suna kalubalantar jam’iyyar daga cire su daga yin takara a mazabu.

Tuni dai Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa 22 ga watan ga watan Satumba mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *