June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Kama wadanda suka rushe ofishin jakadancin Nigeria.

1 min read

Shugaban Ghana ya bai wa gwamnatin Najeriya tabbacin kama mutanen da ake zargi da rusa wani ginin ofishin jakadancin Najeriya a birnin Accra a ƙarshen makon jiya.

Shugaba Nana Akufo Addo, yayin zantawa da takwaransa Muhammadu Buhari ta wayar tarho ranar Talata, ya amsa cewa an yi kuskure wajen rusa ginin da ke cikin ofishin jakadancin Najeriya a ƙasarsa.

Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa shugaban na Ghana ya kuma nemi afuwar Najeriya kan wannan abu.

Rusa ginin da wasu mutane suka yi ranar Asabar a Accra, babban birnin Ghana, ya janyo ɓacin rai da kuma sake tayar da batun rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Al’amarin dai ya janyo kiraye-kiraye a Najeriya cewa gwamnati ta ɗauki matakin ramuwar gayya kan wannan abu da suka bayyana da “cin fuska ga Najeriya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *