April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana Nigeria ce-ce-ku-ce na Kara daukar sabon salo akan Hajjin bana.kan

2 min read

Masu ruwa da tsaki akan ayyukan Hajji da Umara a Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu dangane da matakin da hukumomin kasar Saudiyya su ka dauka na takaita aikin Hajjin bana ga mazauna kasar kawai saboda matsalar annobar cutar coronavirus.

Ranar Litinin 22 ga watan Mayu ne mahukuntan kasar Saudi Arabia suka sanar da wannan mataki da suka dauka, hakan dai na nufin cewa babu aikin Hajji ga dukkanin bakin Alhazai da ke halartar gudanar da wannan muhimmiyar ibada daga kasashen duniya.

Kimanin Alhazai dubu 100 ne ke halartar aikin Hajji daga Najeriya a kowacce shekara, walau ta hannun hukumomin Alhazai na jihohi ko kuma ta kamfanoni masu zaman kansu da ke shirya tafiye-tafiyen aikin Hajji da Umara.

Alhaji Umar Labaran Danga, shugaban daya daga cikin irin wadannan kamfanoni a jihar Kano ya ce, matakin da hukumomin Saudiyya suka dauka sanadiyyar annobar cutar coronavirus ya kara jefa harkokinsu cikin rudani.

A na su bangaren, Malaman addinin Islama na cewa, batun hana ko takaita mahalarta aikin Hajji saboda yanayin annoba, irin wannan yanayin na cikin kundin tarihi don haka babu abinda maniyyata zasu yi sai dai su yi hakuri, a cewar Malam Muhammad Mustafa Dandume.

Yanzu dai maniyyata da sauran ‘yan Najeriya na dakon hukumomin kula da ayyukan Hajji a kasar kan mataki na gaba game da wadanda suka fara biyan kudaden su.

A hannu guda kuma kamfanonin da ke hada-hada a wannan fanni na sauraron samun tallafi daga gwamnati domin su sami sukunin farfadowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *