July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Barcelona za ta sayar wa Juventus Arthur a kan £72.5m, Carvalho ya ƙulla yarjejeniya da Leicester

2 min read

Juventus ta amince ta biya euro 80m domin karbo dan wasan Barcelona mai shekara 22 dan kasar Brazil, Arthur – Amma dole ta rarrashe shi kafin ya koma can. (Sky Sports)

Dan wasan tsakiya na Portugal William Carvalho, mai shekara 28, ya cimma yarjejeniya daLeicester City, abin da ya rage kawai shi ne kungiyar ta Gasar Firimiya ta daidaita da Real Betis kan farashinsa(Marca)

Crystal Palace tana dab da da kammala sayen Nathan Ferguson bayanWest Brom ta tabbatar cewa dan kasar Ingila mai shekara 19 ya ki amsa tayin sabunta kwangilarsa. (Guardian)

Ana sa ran Arsenal za ta amince da tsawaita kwangilar dan wasan Portugal Cedric Soares wanda ta karbo aronsa dagaSouthampton kuma tana so ta sayi dan wasan mai shekara 28 gaba daya idan aka bude kasuwar musayar ‘yan kwallon kafa. (ESPN)

Ana sa ran dan wasan Ingila Andy Carroll, mai shekara 31, zai tsawita kwangilarsa da shekara daya a Newcastle United(Chronicle)

West Ham, Rangers da kuma AZ Alkmaarsuna son dauko dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Dion McGhee, dan shekara 19(Manchester Evening News)

Mamallaka West Ham suna son sayar da kungiyar bayan rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke Hadaddiyar Daular Larabawa tana son sayen kungiyar. (Star)

Watakila dan wasanArsenal dan kasar Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 19, ba zai buga sauran wasannin kakar wasa ta bana ba sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa lokacin atisaye. (Mirror)

Rennes ta nemi bai wa Monaco euro 15m don dauko dan wasan Faransa Benoit Badiashile, mai shekara 19. (RMC Sport – in French)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *