June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Isra’ila za ta kara mamaye wani yankin Falasdinawa

2 min read

Fiye da ‘yan majalisar Birtaniya 240 da ‘yan majalisar dattijan kasar sun rattaba hannu a wata wasika da ‘yan majalisun Tarayyar Turai fiye da dubu daya suka sanya wa hannu da ke Allah wadai da wani shirin Isra’ila na mamaye wasu yankuna na gabar yamma ta kogin Jordan.

Ministocin gwamnatin Isra’ila na iya fara mahawara kan aiwatar da wannan shirin nan da mako mai zuwa.

Wasikar ta fito karara ta na bayyana hadarin da ke tattare da daukan wannan matakin da Isra’ila ke son yi, wanda zai kwace kashi 30 cikin 100 na gabar yamma da kogin Jordan.

Wasikar ta nemi shugabannin kasashen Turai su dauki kwarararn matakai domin hana Isra’ila daukan wannan matakin, wanda suka ce zai kawar da sauran damar da ake da ita ta zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Yahudawa.

Cikin ‘yan majalisar Birtaniya da suke mara wa wannan wasikar baya akwai tsofaffin shugabannin jam’iyyun Conservative da na Labour kamar Lord Howard da Lord Kinnock, da kuma tsohon shugaban Kungiyar NATO Lord Robertson da ‘yan majalisa 35 na jam’iyyar Labour mai adawa.

Akwai kuma wasu tsofaffin ‘yan majalisar kasar Isra’ila da ke goyon bayan wannan yunkurin – kuma sun fito fili suna goyon bayan nemo wata hanya mafi adalci da za a bi wajen warware wannan matsalar.

Falasdinawa na kallon yankin a matsayin wanda za su shigar da shi cikin sabuwar kasar Falasdinu, kuma sun ki amincewa da yunkurin kwace shi da Isra’ila ke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *