June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jihar Kano dake arewacin Nigeria na fama da matsalar Ruwan Sha.

2 min read

Rohotanni daga wasu daga cikin kananan hukumomin Jihar Kano,na nani da cewa da yawa daga cikin na fama da matsalar karancin  ruwan sha musamman a wannan yanayi da ake fama da annobar Coronavirus a duniya baki daya.

Unguwannin Dorayi Babba da Dorayi Babba Yamadawa da Gwammaja da Rijiyar Lemo da Kurna da Gwauron Dutse da Sheka da sauran unguwanni duk musalai ne na unguwannin da abin shafa kai tsaye.

Kamar yadda rohannin suka nuna cewa da yawa daga cikin mazauna irin wannan unguwannin ko kadan ba sa samun ruwan fanfo wanda alhakin gwamnati ne,na  samarwa  al’umma ruwan fanfo,kamar yadda yake tsarin abubuwan marewa rayuwa.

Rashin ruwan fanfo na hadda sawa jama’a matsaloli iri-iri wanda a karshe al’umma kan yi amfani da gurbataccen ruwan sha, haka kuma hakan kan  haifarwa jama’a cututtuka da dama.

A Wasu unguwannin dogon layin diban ruwan na daukar sabon salo inda zaka tarar da wasu guraren kusan botikan diban ruwan kan kwana a layin ruwan musamman ma yadda hakan ke haifar da fada ce –fada ce a tsakanin al’umma.

Wasu ‘Yan Mata a unguwar Rijiyar Lemo sun sun shaidawa jaridar Bustandaily cewa sukan bama su san da wata hukumar samar da ruwan sha ba balle ma a zo maganar karfar harajin gwamnati na wato kudin ruwan sha da hukumar take karba.

A yayin da Jaridar Bustandaily,tayi kokarin jin ta bakin hukumar samar da ruwan sha ta Jihar Kano Ruwasa, domin jin ta bakin su,sai duk Karin da Mukai na jin tabakin nasu amma abin ya faskara sakamakon rashin samun daya daga cikin jami’an hukumar.

Sai wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa da yawa daga cikin kayan aikin hukumar da kuma wasu daga cikin matatun ruwan ba sa aiki yadda ya kamata.

Ko yaushe ne talakawan Nigeria zasu fara kurbar roban dumukuradiyya wanda yau shekara ashirin da daya kenan da komawar Kasar mulkin farar Hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *