July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu annobar Corona a duniya za su kai miliyan 10 zuwa makon gobe – WHO.

1 min read

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce tana tsammanin adadin masu dauke da cutar korona zai kai miliyan 10 a fadin duniya nan da makon gobe.

“An bayyana wa WHO akwai sama da mutum miliyan 9.1 da ke fama da cutar a yanzu, kuma sama da 470,000 sun mutu a duniya,” kamar yadda shugaban hukumar Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya shaida wa maneman labarai a Geneva.

“A watan farko na barkewar annobar, kasa da mutum 10,000 ne suka kamu, amma a watan da ya gabata kimanin mutum miliyan 4 ne aka ba da rahoton kamuwarsu.

“Muna zaton masu dauke da cutar za su kai miliyan 10 nan da sati mai zuwa.”

Ya kira wannan lamari “wata tunasarwa mai daci don bukatar daukar matakin gaggawa da za mu iya mu takaita yaduwar cutar da kuma ceton rayuka”.Article share tools

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *