September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan majalisar Najeriya zasu dauki matakin ramuwa kan Ghana

2 min read

Yan majalisar Najeriya sun nemi a dauki matakin ramuwar gayya kan kasar Ghana bisa ruguza wani ginin ofishin jakadancin kasar a ranar Lahadi.

Dan majalisa Yusuf Buba shi ne shugaban kwamitin harkokin kasashen waje a majalisar wakilan Najeriya ya ce a wani zama da suka yi ranar Talata tare da ministan harkokin wajen kasar da sauran masu ruwa da tsaki, ministan ya ce Ghana ta nemi ahuwa kan abin da ya faru.

Sai dai kwamitin ya ce neman ahuwar kawai ba zai wadatar ba tare da zayyana sharudan da ya wajaba Ghana ta cika kafin a karbi ahuwar tata.

Yusuf Buba ya shaida wa BBC cewa idon Ghana na son a yi mata ahuwa “sai ta sake gina inda aka ruguza wa Najeriya.

Kuma sai an binciko su wanene suka aikata wannan laifi an mika wa Najeriya su domin su girbi abin da suka shuka”.

Bisa yarjejeniyar Geneva inda aka ruguza daidai yake da gidan shugaban kasar dan haka mallakar Najeriya ne , in ji Yusuf Buba.

Ya kuma ce “wasu na cewa wai ginin ya wuce lokacin da ka’idar mallakar kasa a Ghana na shekara 50, sam ba haka bane a 1986 aka bai wa Najeriya ginin kuma lokacin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo aka sake biyan wasu kudade kan ginin don haka bai fi shekara 30 cikin 50 da aka ka’ide.”

To amma fa matukar Ghana ba ta cika wadannan sharuda ba dai dai yake da ta ce a dauki matakin ramuwa kan wannan batu, ya kara da cewa.

A ranar Lahadi ne dai aka je da motar ruguza gini aka rusa wani bangare na ginin ofhsin jakadancin Najeriya da ke Ghana abin da Yusuf Buba ya ce tuni ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *