May 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria ta rabi biyu sakamakon rikicin shugabanci

2 min read

Sanarwar da shugaban APC na riko Mr Ntufam Hilliard Etagbo Eta da Sakataren riko Waziri Bulama suka sanya wa hannu ranar Laraba da almuru ta bayyana cewa “yaudarar” shugaban kasar aka yi ya amince cewa Mr Giadom ne sabon shugaban riko na jam’iyyar.

“Muna so mu bayyana ƙarara cewa mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa sun yi amannar cewa an bai a shugaban kasa gurguwar shawara ko kuma an yaudare shi ya amince da haramtaccen taron da wani mai suna Victor Giadom ya kira ranar 25 ga watan Yuni, 2020,” in ji sanarwar.

Ranar Laraba Shugaba Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam’iyyar APC na kasar.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Laraba da yamma.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai halarci taron da Victor Giadom ya kira ranar Alhamis, wanda za a gudanar ta bidiyo, tare da sa ran cewa gwamnonin jam’iyyar da shugabannin majalisar dokoki na APC za su halarci taron.

A makon jiya ne jam’iyyar APC ta bayyana Sanata Abiola Ajimobi a matsayin wanda zai maye gurbin Adams Oshiomhole, a matsayin shugabanta na riƙo bayan wata kotu ta dakatar da Mr Oshiomhole.

Sai dai jam’iyyar ta amince Mr Eta ya rike masa kujerar har lokacin da zai samu sauki daga rashin lafiyar da ake fama da ita.

Masharhanta a Najeriya irin su Dr. Abubakar Kari sun bayyana matakin da Shugaba Buhari ya dauka na goyon bayan Mr Giadom a matsayin mai cike da ban mamaki da kuma ɗaure kai.

Don kuwa a cewarsa: “sanarwar, wani babban al’amari ne kuma tasirin da za ta iya yi yana da girman gaske”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *