June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Liverpool ta lashe Premier League bayan shekara 30.

1 min read

Liverpool ta kawo karshen shekara 30 da ta yi tana jiran lashe Premier League, bayan da Chelsea ta doke Manchester City da ci 2-1 ranar Alhamis.

Chelsea ta karbi bakuncin City a wasan mako na 31, inda kungiyar Stamford Bridge ta fara cin kwallo ta hannun Pulisic.

Daga baya City ta farke ta hannun De Bruyne sannan Chelsea ta kara na biyu a bugun fenariti ta hannun Willian.

Daman kuma kungiyar da Jurgen Kloop na bukatar cin wasa daya a damka mata kofin Premier na bana sai ga Chelsea ta yi mata aikin.

Wannan shi ne kofin Premier na farko tun bayan shekara 30 da ta ci a 1989-90 kuma na 19 jumulla.

Cikin shekara 30 din Liverpool ta kashe fan biliyan 1.47 wajen sayen ‘yan wasa 239 da kuma koci tara da suka ja ragama kawo yanzu.

Liverpool ta bai wa Manchester City tazarar maki 23, kuma saura wasa bakwai aka damka mata kofin na bana.

Jurgen Klopp ya zama dan kasar Jamus na farko da ya lashe kofin Premier League.

Liverpool a kakar bana idan ka kwatanta da 29 da ta yi a baya
2019-20(1990-91 to 2018-19)
28Yin nasara19.57
2Canjaras9.72
1Losses9.14
70Kwallayen da ta ci65.45
21Kwalayen da aka zura mata38.83
86Maki da ta samu68.57

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *