September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zahradeen Sani Na fi so na fito a matsayin mugu a film.

2 min read

Shahararren ɗan wasan Kannywood Zahradeen Sani Owner ya ce yana jin daɗin tuɓe rigarsa a duk lokacin da yake wasan a fim.

Tauraron ɗan wasan ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC a shafinmu na Instagram ranar Alhamis.

Ya ce hakan yana da dangantaka da yadda yake yawan yin atisayen motsa jiki wato gym, kuma tuɓe riga wani salo ne nasa, kamar yadda tauraron fim ɗin Indiya Salman Khan yake yawan yi a fina-finan Bollywood.Tsallake Instagram wallafa daga bbchausa

Zahradeen ya ce ya fara fitowa a fina-finan Hausa ne a shekarar 2003 a wani fim mai suna Makamashi.

Kazalika tauraron ya ce Ali Nuhu ne mai gidansa a Kannywood saboda shi ne ya fara taimaka masa kuma ya yi jagora masa jagora a lokacin da ya fara shiga harkar fim.

Fim ɗin Daga Ni Sai Ke, shi ne wanda ɗan wasan ya fi so a cewarsa, sannan ya ce ya yi fina-finai kamar 50 zuwa 60.

Har wa yau, Zahradden ya ce ya fi son ya fito a matsayin mugu (boss) sabanin wasu abokan sana’arsa.

Haka zalika ya ce bayan sana’ar fim ya ƙware a sana’ar ɗinki (tela), sai dai ya yi ritaya daga wannan sana’ar a shekarar 2004, amma yana da shagunan ɗinki da ya mallaka a halin yanzu.

A ƙarshe ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta a arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *