June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A yau ake bikin Ranar ‘yan kwaya ta duniya.

1 min read

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar Yaki da shan Kwaya da kuma safararta. Taken ranar na bana shi ne ”Ilimi mai inganci don samun kula mai kyau,” wato “Better Knowledge for Better Care.”

An kirkiri taken na bana ne don inganta fahimtar yadda matsalar kwaya take a duniya da kuma neman hadin kai kan yadda za a yi yaki da hakan don magance illolinta ga lafiya da kuma tsaro.

Arewacin Nigeria dai Jihar Kano ce ke zaman na daya game da yawan matasan dake shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar dukk da cewa gwamnatoci na ta aiki dare da rana wajen magance matsalar.

Ko da yake dai jaridar Bustandaily ta jiyo ta bakin wasu ‘yan kwaya suna bayanin yadda suke ta’ammali da wadannan kayan maye,sai kuma sun ce rashin aikin yi ne ke sanya su make-maken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *