December 11, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An bude cibiyoyin rijistar shirin gwamnatin tarayya na Npower kyau.

2 min read

Matasan karamar hukumar Gwale zasu gudanar da rijistar shirin gwamnatin tarayya Npower kyauta bayan da wani matashi Kwamared Aliyu Yhaya Dorayi ya kaddamar da rabon form a yau Alhamis.

Taron kaddamar da shirin ya sami halartar Farfesa Ibrahim Mu’azzam mai Bushira ya ce irin wadannan matasa al’umma take da bukata a halin yanzu, domin komai na rayuwa yayi tayi wahala ga matasan a dan haka akwai bukatar samarwa da al’umma cigaba hanyoyin dogaro da kai.

Ya kuma kira ga matasa dasu tashi tsaye wajen neman ilimin addini dana zamani tare da neman na kansu ta hanyar koyan sana’o’in dogaro da kai.

Ko da yake jawabinsa shugaban kwamitin amuntattu na kungiyar Dattawan Arewa wato Northern Nigerian Elders Alhaji Nastura Ashir Shareef wanda ya sami wakilci ya bayyana kira matasa dasu lura da dukkan ka’idojin da aka shinfida kafin rubuta bayanan su a na’ura mai kwakwalwa.

A nasa jawabin kwamared Anas Jaddah bayyana jin dadinsa da yadda manyan mutane suka halarci taron cikin su hadda Dakta Sa’idu Ahamd Dukawa dake sashen Kimiyar Siyasa a Jami’ar Bayero Kano, kuma Dakta Usman da sauran manyan baki dama.

Da yake nasa jawabin kwamared Aliyu Yahya Dorayi ya ce ganin yadda ‘yan Kudancin Kasar nan ke barinmu a baya,ya sanya suka ga da cewar tallafawa matasan domin ganin jihar Kano ta sami kaso mafi rin jayi wajen samun wannan dama wanda a baya damar ta kwace wa jihar kano.

Daga cikin cibiyoyin da aka ware dai sun hadar da-;Dorayi Sabon titi da kuma Kabuga wanda duk wanda ya sami form to shi ne tikitin sa na zuwa wajen rijistan wanda aka ware guda 500.

3 thoughts on “An bude cibiyoyin rijistar shirin gwamnatin tarayya na Npower kyau.

  1. ?????? ???? ???????? ??? ?????? ?????? ?? ?????? ???? ???? ???? ??? ????? ?????? ???????? ?????? ???? ????? ?? ??????

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *