An samu raguwar shan kwaya a Jihar Kano.
2 min read
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Kano Dr. Ibrahim Abdul ne ya shaida wa BBC hakan a wata hira ta musamman albarkacin ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta duniya wato World Drug Day.
Dr. Ibrahim Abdul ya ce sun kama tan bakwai na kwaya cikin da tsakanin da jihar ta kasance karkashin dokar kullen cutar korona.
“Mu mun dauka da farko tun da an kulle gari to ba za a samu kamu mai yawa ba, abin mamaki har ofisoshin da suka kasance a rufe an mayar da su wajen shan ƙwaya, kamar ofisoshin gwamnati tun da sun ga ba mutane a wajen
”An samu ƙarin irin ƙwayoyin da matsa ke hadawa da kansu tun da samu a kemis ya yi wahala don an rufe shaguna.
Ya ce cikin matakan da suke dauka sun hada da na wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fada a taken wannan shekara cewa a bi wato amfani da ilimi.
‘Ya kamata a fara koyar da illar shan kwaya a jami’a a Najeriya’
Yadda na daina shan ƙwaya har na kafa ƙungiyar yaki da ita
”Amfani da ilimin nan ya sa muka samu wani mutum da ya dauko kilo 233 na kwaya daga jihar Ondo a Kudancin Najeriya, wanda ya aike shi din kuma yana garin Azare a jihar Bauchi, sai muka yi amfani da ilimi muka dauko na Bauchin muka hada da na Ondon muka kai su kotu,” in ji shi.
Dr Abdul ya ce ya yi nasarar cafke shi na Bauchin wanda dama ya gagari hukuma wajen kamawa, kuma babu wani dan kwaya da ya kai shi shahara a jihar Bauchin.
Kalubalen Hukumar
Dr Abdul ya ce kalubalen hukumar sun hada da:
Karancin ma’aikata da ba za su iya zagaye dukkan kananan hukumomin jihar 44 ba
Gidajen yari ba sa karbar mutane saboda annobar nan, ko da an yanke wa mutum hukunci sai dai a ajiye shi a nan.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar Yaki da shan Kwaya da kuma safararta. Taken ranar na bana shi ne ”Ilimi mai inganci don samun kula mai kyau,” wato “Better Knowledge for Better Care.”
An kirkiri taken na bana ne don inganta fahimtar yadda matsalar kwaya take a duniya da kuma neman hadin kai kan yadda za a yi yaki da hakan don magance illolinta ga lafiya da kuma tsaro.