September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyoyin Mata Sun Bukaci hukuncin Kisa Kan Masu Fyade

2 min read

Gamayyar kungiyoyin mata a jihar Neja da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya sun gudanar da wata zanga-zangar lumana, domin nuna takaicinsu a kan yadda ake kara samun yawaitar fyade a kasar.

Matan dai sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar da ke Minna inda suka mika wata takarda da ke nuna bukatar ganin an yanke hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.

Jagorar zanga-zangar Dr. Aisha Salihu Lemu, ta ce sun zo ne domin rokon gwamnan jihar Neja akan ya dauki matakin yanke hukuncin kisa kan masu aikata laifin fyade.vhugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta jihar Neja, Mary Noel Barje da ‘yar majalisar dokokin jihar Honarable Binta Mamman suna daga cikin wadanda suka gudanar da wannan zanga-zanga, su ma sun nuna takaicinsu kan karuwar fyade tare da kuma yin kira da a samar da dokar hukuncin kisa akan masu aikata wannan mummunar dabi’ar.

Sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, shine ya karbi wadannan mata kuma ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta hada hannu da kungiyoyin fafutuka domin yaki da aikata laifin fyaden.

Wasu alkaluma da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fitar kwanan nan sun tabbatar da cewa an samu korafin laifin fyade har guda 791 daga watan Janairu zuwa watan Mayu na

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *