Sai kowa ya gyara tsakaninsa da Allah komai zai dawo dai a Nigeria iji liman.
1 min read
Limamin Masallsacin Juma’a na Bilal Bn Rabah dake Jihar Jigawa,Dakta Ahmad Isma’il yayi kira ga al’ummar musulmi dasu dage wajen bin dokokin Allah Ubangiji ma daukakin Sarki domin samun saukin matsalolin rayuwa da al’umma ke fuskanta a halin yanzu.
Dakta Ahmad Isma’il yayi wannan kira ne ta cikin Hudubar Sallar juma’a da ya gabatar a masallacin dake Dutse a Jihar Jigawa.
Shehin Malamin ya kuma ce annobar Corona gaskiya ce, kuma aya ga musulmi ya san cewa Allah yana sane da irin manyan zunubai da al’umma ke tafkawa batare da tuba gareshi ba.
Dakta Ahmad Isma’il ya kuma ce gwamnati da sauran masu hannu da shuni dasu samarwa al’umma abubuwa na yau da kullum,inda ya ce akwai lada mai yawa da Allah yayi alkawarin bawa mutanan da suka sa daukar da Dukiyar su ta hanyar da ya da ce.
Limamin ya ja hankalin jami’an tsaron kasar nan dasu guji karbar nagoro a hannun al’umma, dan kuwa amanar da Allah ya dankamusu na kare rayuka da dukiyar al’umma sai sun amsa tambaya akai.