September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A Jihar Kano a Tarayyar Nigeria annobar Corona na dab da Sallama daga Jihar.

1 min read

Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta yi ikirarin cewa babu mutumin da ya kamu da cutar korona a jihar ranar Juma’a.

A sakon da ma’aikatar lafiyar jihar ta wallafa a shafinta na Twitter da tsakar daren ranar, ta ce cikin ba a samu ko da mutum daya da ya harbu da cutar ba cikin mutum 154 da aka yi wa gwaji ranar

Ta kara da cewa an sallami karin mutum 25 bayan sun warke daga cutar, don haka yanzu masu dauke da cutar jumulla su ne 322 inda kuma cutar ta yi ajalin mutum 51.

A makon jiya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ta Kano ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalinkashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.

Tun da fari, Ministan Lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *