April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abin da ya sa ban yanke shawara kan zaɓen 2023 ba

2 min read

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce har yanzu bai yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugabancin kasar ba a zaben 2023 mai zuwa sabanin jita-jitar da ake yadawa.

Ya ce ya damu kwarai kan kalubalen da kasar ke fuskanta a bangaren lafiya da kuma tattalin arziki a yanzu.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya yi tsokaci a karon farko kan dakatar da Adam Oshiomhole daga shugabancin kwamitin kolin jam’iyyar tasu ta APC.

A ranar Alhamis ne majalisar zartarwar jam’iyyar ta ruguje shugabancin kwamitin kolin a wani zaman gaggawa da ya gudana.

Sauyin da zan kawo don gyara jam’iyyar APC – Mai Mala Buni
Tinubu ya ce ana kassara APC saboda zaben 2023
Buhari ya rushe shugabancin APC ya naɗa gwamnan Yobe shugaban kwamitin riƙo
Matsayar Buhari ‘koma-baya ce ga su Oshiomhole da Tinubu’
Wanda ake kallon wannan mataki a matsayin wani koma baya ga burin Tinubu na takarar shugabancin kasar saboda kusancinsa da Adam Oshiomhole.

Tinubu ta cikin sanarwar ya ce, “Ga wadanda ke fadi tashi suna yada matakin shugaban kasa da kuma taron majalisar zartarwa suka kawo karshen burin siyarsar da suke cewa ina da ita na 2023, to ina tausaya musu.

Ni dai mutum ne wanda ba shi da hangen nesa ko kuma hikimar siyasa da kuke ikirarin kuna da ita, dama kun riga kun fara gina kabarin burin siyasa ta wanda zai mutu a 2023, duk da cewa har yanzu ban ma yi kudinba”.

Sanarwar ta kara da cewa: “A wannan mawuyacin hali da ake fama da COVI-19 kuma matsin tattalin arzikin da ta kawo wanda yake shafarmu, ba zan iya yin hange irin wanda kuka yi ba.

Ban yanke shawara kan zaben 2023 ba saboda halin da muke ciki a yanzu ma ya ishe mu.”

“A wannan lokaci, ban mayar da hankali kan siyasar da ta shafi 2023 ba.

Abin takaici ne tare da nuna rashin nuna dattako yadda jama’a ke wani irin tunani a daidai lokacin da ake fama da matsala a bangaren lafiya da na tattalin arziki” kamar yadda sanarwar ta ruwaito Tinubu na fada.

Cikin yan watannin da suka wuce, na dukufa wajen tunanin manufofin da zasu taimakawajen gina Najeriya

“Abin da zan yi ko wanda ba zan yi ba nan da shekara uku masu zuwa wani lamari ne da ba shi da tabbas idan aka yi la’akari da halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *