An gudanar da bikin Babban dan Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam a yau a Birnin Tarayyar Abuja.
1 min read
Salim Jafar Mahmud Adam shi ne babban dan marigayin wanda a yau Asabar aka gudanar da bikin sa.
Duk da cewa iyayen ango sun sanardar da cewa babu taron daurin aure saboda annobar covid 19,amma al’umma sun yi tattaki zuwa Abuja domin shaida wannan daurin aure.
Abokan marigayi Sheikh Jafar da dama sun halarci Abuja a yau din domin tabbatar da wannan aure.
Sheikh Abdullahi Bala Lau wanda shi ne shugaban kungiyar Izala ta Nigeria ne ya daura auren Salim da Naja’atu a Abuja a gaban al’umma da dama.
Daga cikin malaman da suka halarta dai akwai Dakta Bashir Aliyu limamin Masallacin Alfurkan da kuma sheikh Kabiru Gombe da Dakta Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo wanda siriki ga Malam Jafar da kuma sauran mutane da dama.
Salim Jafar Mahmud Adam dai ya auri Naja’atu Abdulaziz Mashi Abdullahi bisa dokoki da shari’ar musulunci ta shinfida