June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

El-Rufai yana so a dinga yi wa masu laifi dandaƙa.

1 min read

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Malam Nasir el-Rufa’i, ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade ita ce yi wa masu aikata laifin dandaƙa.

Malam Nasir ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom ranar Asabar.

An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.

Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *