July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Alhazan Jihar Kano Ta Ce Za Ta Fara Shirin Aikin Hajjin Badi.

1 min read

Kasa da mako guda bayan da hukumomin kasar Saudiyya suka sanar da matakin dakatar da al’umar Musulmin kasashen duniya daga halartar aikin hajjin bana saboda annobar cutar coronavirus, hukumar Alhazai ta jihar Kano a Najeriya ta ce za ta fara shirye-shiryen aikin hajjin badi da zarar ta kammala aikin mayar da kudade ga Alhazan da basu sami sukunin hajjin bana ba, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, sakatren hukumar Alhazai ta jihar Kano ne ya shaida hakan a wata hira da Muryar Amurka.

Fiye da Alhazai dubu 7 daga jihar Kano ne ke sauke farali a kowacce shekara, daga cikin mutune kusan dubu 100 da ke halartar aikin hajji daga Najeriya.Tuni dai masu kula da harkokin ayyukan hajji a Najeriya suka fara tsokaci dangane da wannan yunkuri na hukumomin kasar na fara tsare-tsaren aikin hajjin badi.

Alhaji Usman Darma masani kan ayyukan hajji, ya ce ya yi imanin cewa akwai kyakkyawan zato za a iya samun ci gaba a aikin Hajjin Najeriya bisa ga shirye-shiryen da ake yi yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *