June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A Jihar Sokoto a tarayyar Nigeria mutane 779 suka kamu da Corona.

1 min read

Mutane 779 ne aka ba da rahoton sun sake kamuwa da cutar korona a ranar ranar Asabar. Yanzu yawan masu cutar a Najeriya 24,077.A baya-bayan nan dai Najeriya na fitar da ɗaruruwan alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar, wadda ta fara ɓullar a ƙasar ƙarshen watan Fabrairu.

Alkalumman da hukumar ta fitar sun ce cutar ta sake kashe mutum huɗu a Najeriya ranar Asabar inda yanzu jimillar wadanda cutar ta kashe suka kai 558.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta nuna cikin alƙaluman da ta fitar a daren Asabar cewa har yanzu Lagos, inda cutar ta fi tsanani ce ke kan gaba a yawan mutanen da aka sake ganowa sun kamu, da 285.

Cikin sa’a 24 kuma cutar ta kama mutum 11, a Sakkwato, jihar da a baya ta sanar da cewa babu mai sauran mai ɗauke da cutar.

Bayan Legas, Jihar Rivers ce ta biyu a yawan wadanda suka kamu da cutar a ranar Asabar , wato mutum 68. A Abuja babban birnin Tarayya kuma 60 suka sake kamuwa haka ma jihar Edo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *