Jagoran adawa na Malawi Lazarus Chakwera ya doke Peter Mutharika a zabe.
1 min read
Ya doke shugaba mai ci Peter Mutharika da kashi 58.57 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaben da aka gudanar ranar Talata, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar ranar Asabar
A watan Fabrairu, Kotun kundin tsarin mulki ta Malawi ta doke nasarar da shugaba Mutharika ya samu a zaben watan Mayun 2019, inda ta ce an yi maguɗi a zaben.
Zaɓen zagaye na biyu da aka gudanar makon nan ya raba kan al’ummar ƙasar.
Karo na biyu kenan a Afirka ana soke zaɓen shugaban kasa kan zargin maguɗi bayan Kenya a 2017
Bayan sanar da sakamakon zaɓen a ranar Asabar, Mista Chakwera ya ce nasarar da ya samu “nasara ce ga dimokuraɗiyya da tabbatar da adalci”: yana mai cewa “zuciyata na cike da farin ciki”
Magoya bayansa sun mamaye titunan Lilongwe, babban birnin Malawi, suna wasan wuta da yayata gari da odar mota.