July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Man United ta kai daf da karshe a FA Cup, bayan da ta ci Norwich 2-1.

2 min read

Manchester United ta kai wasan daf da karshe a gasar FA Cup, bayan da ta doke Norwich City 2-1 a ranar Asabar.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Odion Ighalo wanda ke taka rawar gani a kungiyar ta Old Trafford wacce ta tsawaita zaman dan kwallon tawagar Najeriya.

Todd Cantwel ne ya farke wa Norwich, bayan da ya buga kwallo tun daga yadi na 25 ta wuce ta kasan mai tsaron ragar United, Sergio Romero.

Hakan aka tashi wasa kunnen doki 1-1 aka kuma yi karin lokaci, inda suka kammala zangon farko suka fada na biyu duk dai 1-1.

Daf da za a tashi daga wasan ne Harry Maguire ya ci wa Manchester United kwallo na biyu da ya kai kungiyar wasan daf da karshe a gasar bana.

Norwich ta karasa karawar da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Timm Klose, wanya ya yi wa Ighalo keta ta baya.

Wannan ne karo na uku United na zuwa fafatawar daf da karshe a kaka biyar, sai dai wasan da ta buga da Norwich ya nuna United na bukatar bunkasa ‘yan wasanta

Norwich wacce take ta karshen teburin Premier League za ta ci gaba da sa kaimi da sanin halin da za ta tsinci kanta idan an kammala wasannin bana,

Ita kuwa United wadda take fatan lashe FA Cup da Europa League a bana na fatan karkare gasar Premier League cikin ‘yan hudun farko domin ta je Champions League a badi.

Norwich za ta je gidan Arsenal a gasar Premier ranar Laraba, ita kuwa Manchester United za ta ziyarci Brighton.

Wasu batutuwan tarihi:
Manchester United ta kai wasan daf da karshe sau 30 a FA Cup, ta yi hakan fiye da kowacce kungiya a gasar.
Manchester United ta ci wasa 11 daga 13 da ta yi a waje a gasar.
Norwich ba ta ci wasa ba a takwas baya da ta buga a FA Cup, tun bayan da ta doke Burnley 4-1 a Janairun 2012.
Kocin Manchester United, Solskjaer shi ne na farko da ya sauya ‘yan wasa shida a wasa a tarihin kwallon Ingila.
Dan wasan United, Ighalo ya ci kwallo a kowanne wasa uku da ya fuskanci Norwich City.
Ighalo ya ci kwallo a wasa hudu da ake fara karawa da shi a Manchester United.
Wannan ne karon farko da dan kwallon Norwich City, Klose ya karbi jan kati tun wanda aka yi masa yana Wolfsburg a karawa da ta yi da Hannover a Bundesliga a Agustan 2013.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *