June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban Kasar Amurka Trump ya goyi bayan masu nuna wariyar launin fata

1 min read

Shugaban Amurka Donald Trump ya saka wani hoton bidiyo da ya haifar da matsala, bayan da ya nuna wani mai goyon bayansa na fadin farar fata na da karfi a duniya.

Shugaban na ci gaba da fuskantar suka musamman daga kungiyoyin kare bakake da ke cewa ana nuna musu wariya.

Sanata Tim Scott wanda dan jam’iyyarsa ne ta Republican na cikin wadanda suka yi Allah wadai da wannan lamari, kuma ya yi kira ga shugaban da ya sauke hoton bidiyon daga shafinsa na Twitter.

To sai dai fadar White House ta musanta kalaman da ake cece kuce akansu a nata nazarin na hoton bidiyon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *