September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta fitar da Sabbin Matakan kulle takwas.

2 min read

Gwamnatin Najeriya ta sake gabatar wa ‘yan kasar sabbin matakai kan kullen annobar cutar korona.

Hakan na zuwa ne bayan wata guda da bayyana matakin sassauta dokar kulle karo na biyu da kwamitin yaki da annobar korona da shugaban kasar Najeriya ya yi a ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata.

A ranar Litinin ne kwamitin ya kara yin bayani ga ‘yan kasar kan ci gaban da aka samu da kuma sabbin matakan sassaucin da za a dauka a nan gaba.

Mafi yawan sabbin matakan za su fara aiki ne daga daya ga watan Yuli mai kamawa kamar yadda Shugaban kwamitin kuma Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana.

Kwamitin ya ce an samu karuwar kamuwa da cutar cikin gaggawa a Najeriya daga adadin masu cutar 8,915 a ranar 28 ga watan Mayu zuwa 24,567 a ranar Litinin 27 ga watan Yuni.Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar sun haɗa da ɗage haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi amma a lokutan da dokar takaita zirga-zirga ba ta aiki.

A cewar kwamitin dole ne duka tasoshin mota zu zama suna da na’urar auna zafin jiki da kuma tabbatar da ko wanne fasinja sai ya sanya takunkumi kafin ya shiga mota. Za kuma a fitar da wasu dokokin da ake bukatar duka tashoshin kasar su kasance suna bi.

A baya dai kwamitin ya ce an sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin kasar daga karfe 10 na dare zuwa 4 na safiya kuma dokar za ta ci gaba da kasancewa a haka.

Kwamitin ya ce za dokar kasuwanni za ta kasance kamar yadda ta ke a yanzu a fadin kasar.

Kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar korona a Najeriya ya sanar da matakin rufe kananan hukumomi 18 cikin 774 da ke Najeriya.

A cewar kwamitin, wadannan kananan hukumomin su ne suke da kashi 60 cikin 100 na mutum 24,077 da suka harbu da cutar korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *