April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Zaben Somalia Ta Dage Zaben Majalisar Dokokin Kasar

1 min read

Hukumar zabe a Somalia ta ce ba za a iya gudanar da zaben majalisar dokoki kamar yadda aka tsara ba.

Shugabar Hukumar Halima Isma’ila Ibrahim ce ta sanar wa Majalisar Wakilan kasar haka, inda ta ce bambancin ra’ayin siyasa, rashin tsaro, ambaliyar ruwa da kuma matsalar annobar cutar COVID-19, sun sa ya zama dole sai an dage zaben.

A da dai an tsara za a gudanar da zaben ne a ranar 27 gawa tan Nuwamba, yayin da wa’adin shugaban kasa zai kare a ranar 8 ga watan Fabrairun badi, tsare-tsaren da ta ce sun zama dole sai an sauya su.

A halin da ake ciki hukumar ta ce, ana bukatar akalla wata tara nan gaba, kafin a sake wani sabon shiri domin gudanar da zabukan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *