September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rikici ya barke tsakanin Jam’iyya mai mulki a Nigeria da Jam’iyyar adawa PDP.

3 min read

Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP ta nemi Shugaba Muhamamdu Buhari ya fito fili ya nemi afuwar ‘yan Najeriya bisa amfani da kayan al’umma wajen taron jam’iyyarsa.

A makon da ya gabata ne dai wasu hotuna suka nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gudanar da tattaunawa da majalisar kolin jam’iyyar APC da ya kira zuwa fadarsa domin warware takaddamar da ta dabaibaye jam’iyyar.

To sai dai wasu mukarraban shugaba Buhari sun ce ba a fadar shugaban aka yi taron ba inda suka ce an yi taron ne ta kafar intanet, bayan da jam’iyyar PDP ta nemi da shugaban ya nemi afuwa bisa amfani da kayan gwamnati domin biyan bukatar jam’iyya.

A wata sanarwa da PDP ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce ” tabbas a dakin taron majalisar zartarwar Najeriya aka yi wannan taro na keke da keke ba wai ta intanet ba illa iyaka dai an kira wasu mambobin APC ta kafar intanet.”

Sanarwar ta kara da cewa ” abin da ‘yan Najeriya ke nema daga wurin shugaba Buhari shi ne ya nemi afuwarsu bisa anfani da kayan gwamnati inda ba bisa ka’ida. Sannan kuma a guji aikata irin haka a gaba domin gujewa lalata tsarin shugabanci.”To sai dai mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce Buhari na da ikon yin taro a duk wurin da ya ga damar yi a matsayinsa na shugaba kuma jagoran jam’iyyar APC.

Malam Garba Shehu wanda ya shaida hakan a gidan talbijin na Channels a shirin ‘Politics Today’ ranar Lahadi ya ce ” kasancewar shugaba Buhari wanda ya lashe zabe yana da dama shi da jam’iyyarsa su gudanar da taro a fadar shugaban kasa. Jam’iyyar PDP ba ta isa ta yi ba a yanzu tunda ba ta ci zabe ba.”

Mai magana da yawun shugaban na Najeriya ya kara da cewa ” tsarin mulki ya bai wa shugaba Buhari wasu damarmaki da ba kowane yake da su ba. Misali yanzu shugaban PDP ba shi da hurumin da zai nemi daki a fadar shugaban kasa domin ya kwanta. Hakan ba zai yiwu ba tunda ba shi ne a kan mulki ba.”

Har wa yau, malam Garba Shehu ya ce ” annobar korona ce ta tilasta wa shugaba Buhari yin amfani da dakin taron na majalisar zartarwa kuma yana da dama ya yi amfani ko da kuwa da dakinsa ne.”

‘Yan Najeriya dai na ta tafka muhawara kan ko an gudanar da taron na APC a fadar ta shugaban kasa bisa ka’ida, inda wasu ke ganin a sakatariyar jam’iyyar ta APC ya kamata a ce an yi wannan taro.

To sai dai masu magana da shugaban ma ba su amince an yi wannan taro keke da keke ba inda suka ce ta intanet aka yi.

Baya ga batun amfani da dakin taron gwamnati, ‘yan Najeriyar da dama na ta dasa ayar tambaya kan ko dokar takaita zirga-zirga ta jihohi na aiki bisa la’akari da yadda wasu gwamnoni suka halarci taron na APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *