June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An gano wata sabuwar annoba Kasar China.

1 min read

Masana kimiyya sun sake gano wata sabuwar cutar mura a China da ke da yiwuwar zama annobar duniya.

Ta bayyana ne a baya-bayan nan, kuma aladu ne ke ɗauke da ita amma mutane suna iya kamuwa a cewar masanan.

Masu binciken sun damu da cewa cutar tana iya ƙara rikiɗa ta yadda za ta ci gaba da yaɗuwa daga wannan mutum zuwa wancan, har ma ta haddasa annoba a faɗin duniya.

Ko da yake dai, ba matsala ce ta gaggawa ba, amma dai sun ce tana da “dukkan alamomi” na zama mai matuƙar sassauyawa don shafar mutane dalilin da ke wajabta buƙatar yin bibiya ta ƙut-da-ƙut.

Masanan sun ce sabuwar cuta ce, kuma ba lallai ne garkuwar jikin mutane ta iya kare su daga ƙwayar cutar ta bairas ba.

Ƙwararrun sun rubuta a mujallar Proceedings of the National Academy of Sciences cewa kamata ya yi cikin hanzari a ɓullo da matakan taƙaita yaɗuwar ƙwayar cutar a jikin aladu kuma a riƙa matuƙar bibiyar ma’aikatan da ke aiki a masana’antun da ke harkar sarrafa naman aladu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *