June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An zargin Shugaban Majalisar Dattijan Nigeria Ahmad Lawan da wawure wani kaso na samar da aikin yi ga matasa NPOWER

3 min read

Ce-ce-ku-ce ya ɓarke a Najeriya bayan zargin da aka yi wa shugaban majalisar dattijan Batun dai ya janyo tone-tone, musamman ga masu kukan yadda masu mukaman gwamnati kan yi babakere a duk guraben aikin da za a fitar daga ma’aikatu da hukumomi ta yadda `ya`yan talakawa sai dai su ji ana yi.

Ranar Juma’a 26 ga watan Yuni ne aka buɗe kafar shiga cikin sabon shirin ta intanet don bai wa `yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi damar samun tallafi da kuma horo tsawon watanni.

Duk da yake, an sha zargin manyan gwamnatin baya da yin irin wannan babakeren, sai dai wasu masu lura da al`amura kamar Malam Bashir Baba na cewa, har yanzu ba ta sauya zane ba.

“An kai matsayar da, kai da ba kowan-kowa ba, idan kana da ɗa, duk irin kaifin basirarsa, kuma ya yi karatu, ya yi zarra ta hanyar samun kyakkyawan sakamako, to fa maganar samun aikin yi, babu shi.” in ji shi.

Ya ce akasari ‘ya’yan sanannun mutane ake ɗaukowa, a bai wa irin waɗannan gurabe idan an samu, kuma”komai daƙiƙancinsa”.

A cewarsa: “Kuma wannan mugunyar ɗabi’a, ba yadda za a yi ka raba ta da matsalar rashin tsaro da muke fama da ita a ƙasar nan”.

Mai sharhin ya bayyanar cewa mahukunta a Najeriya sun mayar da ƙasar, tamkar wani ramin kura….., Sanata Ahmed Lawan da takwarorinsa ‘yan majalisa da wawure kaso mai tsoka na sabon shirin Npower.

Wasu masharhanta a ƙasar na cewa daɗaɗɗiyar matsalar yin babakere daga manyan jami’an gwamnati a guraben ayyukan yi a ma’aikatu da hukumomi, har yanzu tana ci gaba da addabar Najeriya.

Wasu rahotanni dai a ƙasar sun yi Sai dai, ofishin shugaban majalisar dattijan ya ce zargin da ake yi wa Sanata Ahmed Lawan, ba gaskiya ba ne.

Mataimakin shugaban majalisar dattijan kan harkar hulɗa da jama’a, Alhaji Bashir Jantile rahoton ba komai ba ne face ƙanzon kurege. Ya kuma buƙaci a tuntuɓi ma’aikatar ayyukan jin ƙai don fayyace gaskiyar lamari.

“A tsari na aiki, shi mai girma shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin an tsai da gaskiya. Duk da yake, gaskiya sai Allah!”

Ya nuna cewa irin tsayin dakan shugaban majalisar dattijan kan wasu batutuwa da neman sai an yi gaskiya ne, ke janyo masa zarge-zargen da ake yi.

“Kuma duk wani surutu, ba zai hana shi faɗar a yi gyara ba, ko a yi gaskiya,” in ji Bashir Jantile.

Sai dai wani matashi da ya shafe tsawon shekaru da kammala karatun jami’a ba tare da samun aikin yi ba, ya shaida wa BBC abin da ya kira “wahalar samun aiki a Najeriya”.

Ya ce a lokuta da dama sai mutum ya biya maƙudan kuɗaɗe ko kuma ya san wani fitaccen ɗan majalisa ko wani jami’in gwamnati kafin ya iya samun aikin yi.

A cewarsa: “Wani lokacin ma ana buƙatar naira dubu ɗari biyar har zuwa miliyan ɗaya kai har zuwa miliyoyin, kafin mutum ya iya samun aikin yi.”

Ya ce kimanin shekararsa bakwai da kammala karatun digiri a fannin injiniya amma har yanzu ya gaza samun yi.

“Shin kana neman na abinci ne ko kuwa kana neman tara dubu ɗari biyar ne don sayen aiki?” Matashin ya tambaya. cewa ma`aikatar ayyukan jin ƙai ta keɓe wa `yan majalisar gurbi 50,000 cikin 400,000 da gwamnatin ta tanada a wannan zango,

Sanata Ahmed Lawan dai ya musanta wannan zargi, inda ofishinsa ke alaƙanta batun da “yarfen siyasa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *