Gwamnatin Najeriya Ta Bude Makarantu.
1 min read
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba da umarnin bude makarantu da dage dokar takaita zirga-zirga tsakanin jihohi a duk fadin kasar, a wani mataki na fara sassauta dokar takaita zirga-zirga wacce aka saka domin yaki da annobar Coronavirus.
To sai dai wadanda suke kokarin kammala makaranta ne kawai za su iya komawa, wato yaran da ke ajin karshe a kowane mataki na makarantu wadanda masu yi jarabawa.
An kuma bayyana cewa jiragen sama zasu fara tashi a tsakanin jihohi a kasar, sai dai ba a bayyana lokacin hakan ba.
Shugaban kwamitin babban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na kasar, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a taron da aka yi a Abuja yau Litinin.
Ya bayyana cewa an cimma hakan ne a yayin kashi na 5 na rahoton farko na kwamitin da aka gabatarwa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.
Sai dai gwamnati za ta tsawaita kashi na 2 na sassauta dokar zama a gida na makonni hudu, daga gobe Talata 30 ga watan Yuni har zuwa Litinin, 27 ga watan Yuli.
fatan mu Allah ya yewa bayinsa wannan Annoba. ya Kumamoto basu abinda zasuci su sha
Amin
ok