July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Fasahar 5G Ce Ta Haddasa Annobar Coronavirus?

2 min read

Wani bincike da makarantar Kings College da ke London ta gudanar ya gano cewa, mutanen da ke ziyartar shafukan sada zumunta na Facebook da Youtube domin neman labarai, sun fi fadawa hadarin yarda da ikrarin da wasu ke yi cewa annobar cutar coronavirus manakisa ce aka shirya.

Rahoton binciken ya nuna cewa rukunin irin wadannan mutanen sun fi yin biris da sakannonin da gwammnati ke fitarwa da ke kira ga jama’a su bi matakan kariya a yayin wannan annoba.

Binciken har ila yau, ya gano cewa mutanen su ne za su fi saurin take dokokin kulle da aka saka domin dakile yaduwar cutar ta COVID-19.

A farkon wata nan aka wallafa wannan bincike a mujallar Psychological Medince da ke duba batutuwan da suka shafi yadda dan adam ke tunani.

Masu binciken na Kings College tare da hadin gwiwar wani kamfani mai binciken jin ra’ayin jama’a da ake kira Ipsos MORI, sun duba manakisoshin da ake ta yayatawa yayin wannan annoba.

Fitacciya daga cikinsu ita ce wadda wasu ke yamadadin cewa fasahar sadarwar wayar salula ta 5G ita ta haddasa wannan annoba.

A ‘yan makonnin da suka gabata, an ga yadda wasu suka kakkarya turakun kamfanonin da ke samar da wannan fasaha ta 5G a sassan Birtaniya, abin da ’yan sandan London suka ce, na da nasaba da amincewa da wasu suka yi cewa, fasahar ita ta haifar da wannan cuta ta coronavirus da ke shafar numfashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *